A yau Talata 29/12/2020, yan uwa almajiran Sayyid Zakzaky na da'irar Kaduna sun gudanar da zaman makokin wafatin yar Manzon Allah Sayyida Zahara (As), an fara gudanar da zaman ne da misalin karfe hudu 4:00pm na yanma.
Bayan an gabatar da sallah la'asar sai wakilin yan uwa na da'irar Kaduna Malam Aliyu Tirmizi ya fara gabatar da jawabin sharan fage, in da Malam ya bayyana cewa: idan mutum bai san matsayin Manzon Allah da iyalan sa ba, da falalan su, da darajar su, bazai iya fahimtar Mazalumiyar su ba, a tarihin duniya bawani zalunci da a kayi kamar wanda a kayiwa gidan Manzon Allah (S). An yi zalunci a lokacin Annabawa da ban da ban, amma su zalunci ya tsaya a zamanin su ne, suko Ahlul bayt zaluncin bai tsaya a zamanin su ba, hatta a wannan zamanin in kace kai mabiyin su ne, to zaka hadu da jarabawa. Sannan su wadan can a kwai anbaton su a littatafai, suko Ahlul bayt an boye anbaton su.
Banyan wakilin yan uwa na da'irar Kaduna ya kammala sai a ka gabatar da waken jujayin wafatin Sayyida Fatima, da ga nan a ka mika a bun magana hannun mai jawabi Hujjatul Isalam Malam Isma'il inda ya gabatar da jarabawabi ga mahalar ta taron game da Mazlumiyar da musa'ib da Ahliy Muhammad suka fuskanta a tsawon tarihi.

Malamin ya fara ne da ta'aziya ga Manzon Allah da Iyalan gidan sa, da kuma al'ummar duniya gaba daya, sannan ya ce: farkon Shahada a duniyar Musulunci mace ce, haka ma farkon kare imamanci Sayyida Fatima ne, ba dan tsayuwar Sayyida ba, da baka i sa a wannan zamanin ka kare al'amari ghadeer ba, domin tanayar da zai fara fitowa da ga bakin jama'a shi ne, kai kafi yar Manzon Allah sanin wa ya kamata abi ne, me yasa batayi magana ba. Sannan ya kara da cewa: da wane bai mari Sayyida Fatima ba, da  banu umayya ba su samu damar yanke kan Imam Hussain ba, malam ya bayyana cewa: daga cikin aikin da masu mukin farkon suka yi shi ne yanke albashin talakawa dan suyi mubayi'a a gare su, za mu iya fahimtar haka ne ta yadda suka kwace gonar Sayyida, domin da wannan gonar ne suke taimakon raunana.
Malam ya cigaba da jero falala da darajojin Sayyida Fatima (As), da kuma irin masa'ib din da ta fuskanta.

Bayan kammalawa akayi Addu'a a ka tashi.