Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

An fara Maulidin Sayyida Zahra (as) A Da'irar Kaduna....

Kaduna Press

A jiya Alhamis 21 ga watan janairu, halkar Imam Hassan Almujitafa na Da'irar Kaduna suka fara gudanar da gagarumin Maulidin Sayyida Fatima (as) na shekar 2021/1442Ah.
An gudanar da wannan taron ne a layin chamber barnawa, an fara shi ne da misalin karfe biyu na rana, 3:00pm na rana daidai.
An fara bude taron ne da addu'a, sai karatun Alkur'ani mai girma, sai kuma wake daga shu'ara. Bayan nan sai a ka gabatar da mai jawabi Malam Ahmad Rufa'i, Malamin ya fara ne da salatin Annabi Muhammad (S), da kuma taya mahalarta taron murnar samuwar Shugaban Mata Sayyida Fatima (As). Sannan ya dan yi shinfida game da matsayin Ahlul-Bayt (As).
Sai ya shiga bayani game da falalar Sayyida Zahra (as) da kuma irin mazulumiyar da a ka mata.
Bayan Malamin ya kammala sai a ka gabatar da wakilin yan uwa na garin Kaduna, Malam Aliyu Umar (Tirmizi), in da ya yi takaiceccen ta'aliki.
Daga nan sai a ka gabatar da hakkin shuhada, da kuma kyautan keke napep ga shahidi mai rai na halkar, dhi dai wannan shahidi mai rai ya rasa kafar sa guda ne, sakamakon harin jami'an yan sanda, da suka kaiwa muzahara labbaika Rasulullah  a shekarar 2019, a yan timatir da ke nan bakin dogo Kaduna, san nan a ka yi walima, sai jawabin godiya daga shugaban halkar malama Aisha, sai a ka rufe taro da addu'a. Jama'ar unguwar sun nuna farin cikin su. An kammala taro lafiya, kowa yana sambarka, da fatan ganin na badin-badada.

Kaduna Press
Kd-001/007
©21/1/2021

Post a Comment

0 Comments

Close Menu