Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

AN SABUNTA KIRAN A SAKI ZAKZAKY A DA'IRAR KADUNA.....

Da yanmacin yau Labara 25 ga watan 1 Shekarar 2021 da misalin karfe 06:00pm daruruwa yan'uwa Almajiran Sheikh Zakzaky, na garin Kaduna sun fitowa kan titin gwambe road by logos street dan cigaba da yin kira ga gwamnatin  Buhari da ta gaggauta sakin jagoran harkar musulunci a najeriya Sheikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa, wanda da take fama da rashin lafiya mai tsanani, tsawon shekaru fiye da biyar ba tare da laifin komai ba.
Tun bayan harin Sojojin Najeriya bisa  jararancin yusuf tukur burtai, karkashin gwamnatin Buhari, a ranar 12/12/2015, na kisan mabiyan sa sama da dubu, ciki har da ‘ya‘yansa uku, da kona yayar sa da ranta a gaban sa.
A shekarar 2016 babban Kotun dake Abuja ta wanke shi, tace: baiyi laifin komai ba, asake shi. Gwamnatin taki tayi kunnen uwar shegu da maganar.
In da suka dawo da shi kaduna karkashin Nasiru El rufa'i, su ka fa sabuwar kotu wai suna tuhumar sa da kisan kai, yayin da suke ta ja lokacin na gudanar da wannan shari'a.
Har yanzu dai gwannatin El rufa'i ta kasa gamsar da duniya dalilin kisan kiyashin da sukayi a zaria, da kuma tuhumar da sukewa jagoran harkar musulunci sheikh Ibrahim Zakzaky.

A yau 25 ga watan janairun shekar 2021 a ka cikaga da sauraran wannan kara, in da lauyan gwamnati bayaro dari ya gabatar da shaidu hudu, Shaidun sun hada da ACP Ibrahim Abdul, Col Gideon RTD, da wani yaro dan Gabari da kuma wani mutum da ya ce shi dan Unguwar Aska ne a Zaria City. Sannan Kotu ta bayar da Oda ga Correctional center da su kai Malama asibiti har sai ta warke sannan a mayar da ita. Idan Allah ya kai mu gobe Talata 26/1/202 za a daura daga inda a ka tsaya yau.

©Kaduna press
25/1/2021

Post a Comment

0 Comments

Close Menu