Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

​Iran Ta Yi Maraba Da Shawarar Kafa Kawancen Tattalin Arziki Tsakanin Kasashe 6 Na Yankin


Kaduna Press 

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, Iran tana maraba da shawarar kafa kawance mai karfi na tattalin arziki tsakanin kasashe shida na yankin.

Muhammad Jawad Zarif ya bayyana hakan ne yau a lokacin da yake hanawa da shugaban kasar Azerbeijan Iham Aliyev a birnin Baku fadar mulkin kasar, a wata ziyarar aiki day a fara gudanarwa a yau a kasar.
Zarif ya ci gaba da cewa, Iran ta yi maraba da shawarar da shugaban kasar ta Azerbeijan Ilham Aliyev ya gabatar, ta kafa wani kwance na gungun kasashe shida na yankin, domin gudanar da ayyuka na tattalin arziki a tsakaninsu, wato kasashen Azerbeijan, Turkiya, Iran, Armenia, Rasha da kuma Georgia.
Ministan harkokin wajen kasar ta Iran ya ce yin hakan zai kara karfafa ayyuka a bangaren harkokin kasuwanci da tattalin arziki da cinikayya a tsakanin wadannan kasashe, kuma hakan zai amfanar da dukkanin kasashen yankin ne baki daya.
Shi ma a nasa bangaren shugaban kasar ta Azerbeijan Ilham Aliyev ya bayyana jin dadinsa da yadda Iran ta karbi wannan shawara, kamar yadda kuma ya yaba da irin rawar da Iran ta taka wajen ganin an kawo karshen rikicin da ya faru a watannin baya a tsakanin Azerbeijan da kuma Armenia.
Ziyarar ta Zarif, bayan Azerbeijan za ta hada da kasashen Turkiya, Armenia, Rasha da kuma Georgia.
015
 
 Kaduna Press 
25/1/2021

Post a Comment

0 Comments

Close Menu