Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Wakilan Yan uwa Almajiran Sheikh Zakzaky Na Da'irar Kaduna Sun Kai Ziyarar Jaje Na Kama Almajirai Da A Kayi Gidan Sheikh Dahiru Bauchi Da Ke Askwalaye.....

A yau Lahadi 24/1/2021 Wakilan yan uwa na da'irar Kaduna sheikh Aliyu Umar (Tirmizi) ne ya jagoraci wannan ziyara, Malam Ibrahim, Shehu fandogari tare da Isah Aliyu, sune suka tarbe su. Bayan gaisuwa tare da bayyana makasudin wannan ziyara, sai a ka yi musu jajen abin da ya faru na kwashe almajirai da gwamnatin jahar kaduna tayi. A cikin bayanin wakilan yan uwa na da'irar kaduna, ya bayyana cewa: Manzon Allah (s a w) Yace: zan barmaku Abubuwa
guda biyu masu nauyi wanda in kunyi riko da su a bayana ba za Ku bata, littafin Allah Alkur'ani da Ahlul Bayt (As) tin daga wannan lokacin a ka afkawa Ahlul-bayt, nasan tin da suka taba Ahlul bayt to baza su kyale alkur'ani da makaran tan sa ba, San nan ya ce: a baiwa almajirai hakuri jaraba wace zata wuce, domin bawani wanda ya tabayin addini bilhakki da gaskiya face ya fuskanci jarabawa.
An samu fahimtar juna a wannan ziyara sannan sukayi godiya tare da addu'a ga jagoran harkar Musulunci Sheikh Ibrahim Zakzaky da fatan Allah ya kubuto da shi daga hannun azzalumai.
Suka yiwa yan uwa rakiya har wajen mortar su.

Kaduna Press
 Kd-001/007
©24/1/2021


Post a Comment

0 Comments

Close Menu