Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

YADDA A KA GUDANAR DA MAULIDIN SAYYIDA FATIMA (AS) A HALKAR IMAM HUSSAIN KADUNA.....

A jiya Asabar 23/1/2021 yan uwa almajiran Sayyid Zakzaky na da'irar halkar Imam Hussain kaduna, sun gudanar da Maulidin Sayyida Fatima (As), an fara taron ne da misalin karfe uku 3:00pm na rana, bayan bude taro da addu'a sai karatun Alkur'ani da kuma ziyarar Sayyids Zahra daga daliban fudiyya, dagan sai a ka shiga fagen bege da ga sha'irar. Daga nan sai a ka gabatar da mai jawabi Malama Jamila Auwal Muktar Sahabi, in da ta gabatar da jawabi game da falalar Sayyida Fatima (as), a cikin bayanin ta malama ta fadi cewa: ba wani Annabi da ya zo duniya bace ya fadi falalar Sayyida Fatima da soyayya gareta, sannan ta kara da cewa: Sayyida Fatima Ilimi ce a kan kanta, dole Sister ta tsayu da neman ilimi da ibada, don koyi da Sayyida, duk wance ta kasance ba ta da wannan, to karda ta kira kanta da fatimiyun ko zayyanabiyun, sanan kiyi hakuri da dukkan masa'ib da zai sameki, domin sai ka siffantu da aukan mutun kake zama mai koyi da shi.
A kar she malama tayi kira ga yan uwa mata da su yi wa Kansu tsari na abin da ya shafi ibada.
Daga nan a ka mika abun magana ga wakilin yan uwa na garin kaduna Malam Aliyu Umar (Tirmizi), inda da ya yi gajeren ta'aliki, malam ya fara ne da yiwa Allah godiya da ga nan sai ya dora bayanin sa daga inda malam jamila ta tsaya game da mujahada, akarshe Malam ya yi kira ga yan uwa a kan sauke Hakkin Jagora, a lokaci guda kuma ya yi kira ga gwamnatin Nigeria da ta Gaggauta Sakin Jagoran harkar Musulunci Sayyid Ibrahim Zakzaky da Matarasa malama Zeenatudin wanda take dauke da cutar Covid 19 yanzu haka a gidan kurkukun kaduna, a yayin da yake wannan kiran wakilin yan uwa na Da'iran kaduna Sheikh Aliyu Tirmizi ya sa ka jawabin Sayyed Zakzaky da yake Magana a kan cewa duk wanda bai shirya ba da rai a wannan tafiyar ba yaja baya.
A karshe ya yi Kira ga yan uwa da ke da'iran kaduna da su cigaba da fitowa duk lokacin da a ka yi kira muzaharori babu dare babu rana har sai gwamnati ta saki Jagoran Harkar Musulunci da mai dakin sa. 
Da ga nan kuma yayi Kira ga yan uwa almajiran Sayyid Zakzaky da su bi shawarwarin likitoci na anfani da takunkumi (face max) 😷 duk sanda za a yi wani taro ko muzahara, domin kauce ma sharrin azzalumai, kar su fake da shi su aiwatar da mugun Shirin su a kan yan uwa, sanin  kowa ne a kasar nan Almajirin Sayyid Zakzaky sunfi kowa bin doka.
Sannan a raba walima da kyaututuka, ga iyalan shuhada da mahalarta taron, sannan a kayi addu'a a ka sallami kowa.

Kaduna Press 
©23/1/2021

Post a Comment

0 Comments

Close Menu