Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

An Gana Tsakanin Ministan Tsaron Kasar Iran Da Babban Hafsan Sojojin Kasar Indiya


Kaduna Press 
4/2/2021

Da yammacin jiya Laraba Ministan tsaro na kasar Iran Burgediya Janar Amir Khatami ya gana da babban hafsan sojojin kasar Indiya a safiyar yau Laraba a gefen taron kasuwar baje kolin kayakin jiragen sama na kasar India.

Majiyar muryar jumhuriyar musulunci ta Iran ta nakalto Janar Khatami yana cewa kasashen Iran da Indiya suna da matsayi mai muhimmanci a yankin Asiya don haka akwai bukatar kasashen biyu su yi aiki tare don tabbatar da zaman lafiya a yankin.
A nashi bangaren Bipil Rowaat babban hafsan sojojin kasar Indiya ya godewa ministan tsaron kasar Iran bisa halattar taron bikin baje kolin kayakin jiragen sama na kasar Indiya, wanda alama ce ta kekyawar niyya da kuma damar kara dankon zumunci tsakanin kasashen biyu.
Daga karshen bangarorin biyu sun tattauna hanyoyin aiki tare a bangarori daban daban a tsakanin kasashen biyu.

Kaduna Press 
4/2/2021

Post a Comment

0 Comments

Close Menu