Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

AN SABUNTA KIRAN A SAKI ZAKZAKY A DA'IRAR


Kaduna Press

Da yanmacin yau Alhamis 11 ga watan 2 Shekarar 2021 da misalin karfe 06:00pm na yanma, daruruwa yan'uwa Almajiran Sheikh Zakzaky, na garin Kaduna sun fitowa kan titin Nnamdi Azikiwe Byapass Daura da Gwamna Road, domin cigaba da yin kira ga gwamnatin  Buhari da ta gaggauta sakin jagoran harkar musulunci a najeriya Sheikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa, wanda da take cigaba da tsarewa tsawon shekaru fiye da biyar ba tare da laifin komai ba.Tun bayan harin Sojojin Najeriya karkashin gwamnatin Buhari da ta yi a ranar 12/12/2015, na kisan mabiyan sa sama da dubu, ciki har da ‘ya‘yansa uku, da kona yayar sa da ranta a gaban sa.

A shekarar 2016 babban Kotun da ke Abuja ta wanke shi, tace: baiyi laifin komai ba, asake shi, Gwamnatin taki tayi kunnen uwar shegu da maganar.
In da suka dawo da shi kaduna karkashin Nasiru El rufa'i, su ka fa sabuwar kotu wai suna tuhumar sa da kisan kai, yayin da suke ta ja lokacin na gudanar da wannan shari'a.
Har yanzu dai gwannatin El rufa'i ta kasa gamsar da duniya dalilin kisan kiyashin da sukayi a zaria, da kuma tuhumar da sukewa jagoran harkar musulunci sheikh Ibrahim Zakzaky.
Yanzu haka dai Sheikh Zakzaky (H) yana gidan kurku a nan garin Kaduna, tare da iyalansa, duniya na ta Kira da a sakeshi, amma wannan gwamnatin tana nuna halin ko in kula.

Kaduna press
©11/2/2021

Post a Comment

1 Comments

Anonymous said…
Good yayi kyau
Close Menu