Kd-Press Online 

©25/2/2021

Da yanmacin yau Alhamis 25 ga watan 2 Shekarar 2021 da misalin karfe 06:00pm na yanma, daruruwa yan'uwa Almajiran Sheikh Zakzaky, na garin Kaduna sun fito domin cigaba da yin kira ga gwamnatin  Najeriya da ta saki jagoran harkar musulunci a Najeriya Sheikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa, wanda da take cigaba da tsarewa tsawon shekaru fiye da biyar ba tare da laifin komai ba.


Tun bayan harin Sojojin Najeriya karkashin gwamnatin Buhari da ta yi a ranar 12/12/2015, na kisan mabiyan sa sama da dubu, ciki har da ‘ya‘yansa uku, da kona yayar sa da ranta a gaban sa.

A shekarar 2016 babban Kotun da ke Abuja ta wanke shi, tace: baiyi laifin komai ba, asake shi, Gwamnatin taki, tayi kunnen uwar shegu da maganar.
In da suka dawo da shi kaduna karkashin Nasiru El rufa'i, su ka fa sabuwar kotu wai suna tuhumar sa da kisan kai, yayin da suke ta ja lokacin na gudanar da wannan shari'a.


Har yanzu dai gwannatin El rufa'i ta kasa gamsar da duniya dalilin kisan kiyashin da sukayi a garin zaria, da kuma tuhumar da sukewa jagoran harkar musulunci Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Yanzu haka dai Sheikh Zakzaky (H) yana gidan kurku a nan garin Kaduna, tare da iyalansa, duniya na ta Kira da a sakeshi, amma wannan gwamnatin tana nu na halin ko in kula.

Muzaharar ta daga a dai dai Kaduna Polytechnic, In da ta mike hanya har zuwa shatale talen kasuwar barci.
An yi lafiya an tashi lafiya.

Kd-Press Online 
©25/2/2021