Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

​Iraki:Daesh Ta Kai Hari Kan Cibiyar ‘Yansanda A Lardin Kirkuk


Labaran duniya 
Kaduna Press 
2021-02-06 

Ragowar mayakan kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh a kasar Iraki sun kai hari kan wata cibiyar ‘yan sandan gwamnatin kasar dake a birnin Kirkuk.

Kamfanin dillancin labaran ‘Sabirun News’ na kasar ta Iraki wanda yake karkashin jami’an tsaron kasar ya bada sanarwan cewa ragowar mayakan Daesh a kasar sun kai hari kan wata cibiyar ‘yansandan a daren jiya Jumma’a, sai dai labarin bai bayyana yawan asarori na rayuka da dukiyoyin da aka yi ba, har zuwa lokacin bada wannan labarin.
Tun shekara ta 2017 ne jami’an tsaron gwamnatin kasar ta Iraki, wadanda suka hada da hashdushabi suka sami nasara kawo karshen ikon kungiyar a wasu yankunan kasar Iraki da ta mamaye, amma har yanzun akwai ragowarsu wadanda suke kaiwa jami’an tsaron kasar hare-hare nan da can.
Lardunan da abin ya fi shafa dai a halin yanzu suna hada da Diyala, Kirkuk, Ninawa, Salahuddeen, Ambar da kuma Bagdaza babban birnin kasar.

Kaduna Press

Post a Comment

0 Comments

Close Menu