Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Iran Ba Za Ta Mutunta Yarjejeniyar Nukiliya Ba, Har Sai Amurka Ta Janye Mata Takunkumi

Labaran duniya 
Kaduna Press 

Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya bayyana cewa, Iran za ta dakatar da matakan da ta dauka kan yarjejeniyar nukiliya ne idan Amurka, ta janye mata gabadayen takunkuman data kakaba mata.

Ya kara da cewa ‘’matsayin jamhuriyar musulinci na karshe, shi ne Amurka ta fara dage dukkan takunkuman data kakabawa Iran, sannan Iran ita ma ta kawo karshen matakan data dauka na daina aiki da wasu bangarori da yarjejeniyar ta kunsa.
Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya bayyana hakan ne yau Lahadi, lokacin da yake ganawa da matuka da kwamandojin da mambobin rundinar sojin saman kasar.
Ganawa da manyan sojojin saman kasar, da jagoran ya yi na zuwa ne a zagayowar ranakun cin nasara juyin juya halin musulinci na kasar, wanda a rana irin ta yau ne a shekarar 1979, sojojin saman kasar suka yanke kauna ga mulkin sarki Shah, sukayi kuma sanar da yin mubayi’a ga mirigayi Imam Khomeiny, wanda ya assasa jamhuriyar musulinci ta Iran, shekaru 42 da suka gabata bayan dawowarsa daga gudun hijira. 
024

Kaduna Press 
8/2/2021

Post a Comment

0 Comments

Close Menu