Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Jagora:Ba Abinda Makiya Jumhuriyar Musulunci Ta Iran Suka Iya Da Ita

Kaduna Press 
Labaran duniya
 4/2/2021

Jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullah Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa makiyan JMI, ba abinda suka iya da ita.Tashar talabijin ta Al-Alam wacce take watsa shirye-shiyenta da harshen larabci a nan Tehran ta nakalto jagoran yana fadar haka a safiyar Jiya Laraba, a cikin Husainiyyar Imam Khomaini (q) inda ya yi jawabi ga masu rera wakokin yabon iyalan gidan manzon Allah(s).

Jaronar ya bayyana cewa Fatima Azzarah, (s) diyar manzon Allah (s) wacce aka Haifa a rana mai kama da yau, wato 20 ga watan jamada Thani shekara 5 bayan fara annabci, kekyawar misali ce ga macce, a matsayin mahaifiya, matar aure da kuma mai tarbiyya a addinin musulunci.
Jagoran ya kara da cewa, tarbiyyar mutum musulmi tana faraway ne daga gida kuma a kan mata ne alhakin hakan ya fara sauka.
Dangane da makirce-makircen makiyan JMI da Iran kuma, musamman gwamnatocin Amurka da HKI, jagoran ya kara jaddada cewa, ba abinda za su iya yi da ita da, kuma addinin musulunci.
Ya ce duk tare da makirce makircensu, kasar Iran da kuma addinin musulunci sai kara habaka su yi a duniya.

Kaduna Press 
4/2/2021

Post a Comment

0 Comments

Close Menu