Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Kar ku tursasa wa Shaikh Abduljabbar!

TAKARDAR SANARWAR MANEMA LABARA

Harkar Musulunci a Nijeriya tana sane da cewa gwamnatin jihar Kano a ranar Laraba 03/02/2021, ta hannun Kwamishinan watsa labarai, Muhammad Garba, ta ba da umurnin a rufe masallacin Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara da gidansa da ke Karamar Hukumar Gwale cikin birnin Kano. Kuma kashegari da sassafe, sai ga jami’an tsaro cikin shiri kamar za su yaki, tare da Jami’an tsaron kasa na farin kaya sun isa masallacin da gidansa don tabbatar da wancan umurni.

Kamar yadda gwamnatin Ganduje ta jihar Kano ta ce, wannan umurnin ta ba da shi ne don samar da zaman lafiya a jihar bayan zargin da aka yi wa Shehin Malamin da zagin sahabban Annabi Muhammadu a karatuttukansa na addini, kamar yadda wasu Malaman jihar suka fada.

Amma a bayyane yake cewa, wadannan Malaman da ita gwamnatin jihar Kano da suka zargi Shehin Malamin da zagin Manzon Allah da sahabbansa ba su ba shi damar ya kare kansa ba, kuma ba su nuna takamaime wuraren da ya yi zagin ba a jawabansa. Haka nan kuma ai Shaikh Abduljabbar ya musanta wadannan zarge-zarge a wasu fayafayen bidiyo da suka karade dandalin sada zumunta na zamani, har ma a wata hira da gidan rediyon BBC sashen Hausa suka yi da shi. Ya dage a kan cewa shi fa yana inkarin wasu maganganu ne da suke cikin littafan Sunna wadanda ba kawai sun yi tanakuli da juna ba ne, sun kuma saba da hankali, suna cin zarafin Ma’aikin Allah, amma duk da haka ake jingina su gare shi.

Alal hakika, Harkar Musulunci ta yi tir da wannan mataki na baya-bayan nan na tursasa wa wannan sanannen Shehin Malami tare da bayyana hakan a matsayin wani babban zalunci. Mun yi amanna cewa gwamnatin jihar Kano karkashin Dk. Abdullahi Umar Ganduje ta dauki wannan mataki ne saboda matsin lambar da wasu Malamai da ba sa jituwa da Shaikh Abduljabbar suka yi mata. Amma muna tunatar da ita cewa, wadannan Malaman da take mara musu baya almajiran Ibn Taimiyya ne, wani Malami da aka yi shi a karni na 7, wanda Malami ne mai jawo cece-kuce, wanda kuma kusan dukkan ’yan ta’addan da suke fakewa da Musulunci suna ta’addanci da shi suke koyi. Irin wadannan kungiyoyi ne suke amfani da sunan Musulunci suna kisa da lalata dukiyar duk wani wanda bai da ra’ayi irin nasu, wanda haka shi ne kololuwar rashin kaunar zaman lafiya da wadanda ake da sabanin ra’ayi na addini da su.

Abin sani shi ne gwamnatin da ba ruwanta da addini bai kamata a ga tana marawa wata kungiya ta addini ba, don kuwa hakan karara ya saba wa tanaje-tanajen da ke cikin tsarin mulkin Nijeriya sashi na 38, 39 da 42 da kuma kudurorin Majalisar Dinkin Duniyada na Afrika kan kare hakkin dan Adam. Sannan kuma wannan dakatarwa da aka yi wa Shaikh Abduljabbar ya saba wa doka, saboda ba wata doka da ta mai da gwamnatin jiha ‘Magatakardar’ da za ta iya cewa ga wa’azi mai kyau, ga wa’azi mara kyau. Zai fi kyau ne a ce Gwamnan ya tattauna da Malaman da suke da korafi kan wa’azin Shaikh Abduljabbar, ya nemi su fahimci cewa tunda dai ba tilasta wa kowa yake yi su bi shi ko su ji wa’azinsa ba, to bai kamata a dakatar da shi da karfin gwamnati ba, maimakon haka gara a yi muhawara ta ilimi ce don fahimtar juna.

A karshe muna bai wa masu bin tafarkin Sunna a Nijeriya shawarar su bi hanyar muhawara ne don warware shubuhohin da Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara ke magana a kansu. Amfani da karfi da kuma sharri da farfaganda ba zai taimake su ba. A sarari yake cewa wasu Malaman sun rika yayyanke jawaban Shehin Malamin suna jonawa ta yadda mai sauraro zai zaci cewa Shehin ne ke zagin Manzo da sahabbai, suna kuma yayyada shi a tsakankanin jama’a, suna cewa Shaikh Abduljabbar ya zagi Annabi da sahabbai. Su sani cewa kowane dan Nijeriya yana da damar ya zabi addinin da yake so ya bi. Tursasa wa Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara da mabiyansa ya saba wa kwansitushin din Nijeriya, doka da oda da kuma hakkin dan Adam.

Abin takaici, kai ka ce jiya aka auka wa Shaikh Zakzaky, yau kuma Shaikh Abduljabbar, to hakika Malaman da suka goyi bayan Malaman Salafawa, wadanda ba su yarda da Musuluncinsu ba, sun dauke su Mushirikai ne ma, don su yaki Shaikh Abduljabbar, za su kasance wadanda za a auka wa a nan gaba. Idan ba su manta ba, ba a jima ba da gwamnatin jihar Kaduna ta auka gidan Shaikh Dahiru Usman Bauchi na Tijjaniyya, suka kame daliban da ke gidan. Haka kuma wani Malami Batijjane, Farfesa Ibrahim Maqari ya sha fama da kiraye-kirayen a tsige shi daga Limancin masallacin kasa da ke Abuja. Kukan kurciya dai jawabi ne.

SA HANNU:
IBRAHIM MUSA
SHUGABAN DANDALIN YADA LABARAI
HARKAR MUSULUNCI A NIJERIYA
SKYPE: Ibrahim.musa42
07/02/2021

Post a Comment

0 Comments

Close Menu