Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Kungiyar Kasashen Musulmi Da Azhar Sun Yi Maraba Da Matakin Kotun ICC Kan Laifukan Isra'ila


A cikin bayanan da suka fitar kungiyar kasashen musulmi da kuma cibiyar Azhar sun yi maraba da matakin da kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya ta dauka na yin bincike kan laifukan yakin Isra'ila a kan Falastinawa.

Kungiyar kasashen musulmi ta OIC ta bayyana wannan matsaya ta alkalan kotun manyan laifuka ta duniya da cewa mataki ne mai kyau, kuma tana goyon bayan hakan.

Anasa bangaren babban malamin cibiyar Azhar Ahmad Tayyib shi ma anasa bangaren ya bayyana cewa, matakin na alkalan kotun manyan laifuka ta duniya zai kara fallasa gwamnatin yahudawan Isra'ila, dangane da irin zaluncin da take aikatawa kan al'ummar Falastinu marassa kariya.

Daga karshe ya kirayi bangarori na kasa da su bayar da hadin kai domin ganin an aiwatar da wannan mataki na bincike kan laifukan yakin Isra'ila a kan al'ummar Falastinu.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu