Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Labarin Wasanni: Cinikayyan Yan Wassan Kwallon Kafa

Man City na ci gaba da zawarcin Lionel Messi, Man Utd ta gano dan wasan baya da take son dauka, Chelsea na son David Alaba ya rage kudin da yake son a rika biyansa, da karin labarai kan makomar 'yan kwallo.

Dan wasanInter Milan dan kasar Belgium Romelu Lukaku, mai shekara 27, da dan wasan Southampton dan kasar Ingila Danny Ings, mai shekara 28, na cikin 'yan wasan da Manchester City take son dauka a yayin da kungiyar take neman 'yan wasan gaba. 

Dan wasan Najeriya Shola Shoretire, mai shekara 17, ya sanya hannu kan kwangilarsa ta farko ta kwararrun 'yan wasa a Manchester United, duk da cewa PSG, Barcelona, Juventus da Bayern Munich sun yi tayin daukarsa.


Manchester United tana son daukar dan wasan RB Leipzig mai shekara 21 dan kasar Faransa Ibrahima Konate. Sai dai za ta fuskanci gogayya daga wurin Liverpool da Chelsea.

Chelsea za ta nemi daukar David Alaba ne kawai idan Bayern Munich ta rage kudin da ta sanya a kansa wato £400,000 duk mako. Kwangilar dan wasan na Austria mai shekara 28 za ta kare a Munich a bazara.

City za ta fuskanci kalubale daga Paris St-Germain kan tsohon dan wasan Manchester United Lukaku.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu