Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Majalisar Dokokin Isra’ila Na Zaman Gaggawa Kan Batun Kotun ICC

Labaran duniya 
kaduna Press 
7/2/2021

Kafafen yada labarai na haramtacciyar kasar Isra’ila sun bada labarin cewa firai ministan kasar Benyamin Natanyahu ya kira taron gaggawa na majalisat tsaron kasar don tattauna dangane da anniyar kotun hukunta laifuffukan yaki ta kasa da kasa ICC na binciken laifuffukan take hakkin bil’adama da aka aikata a kasar Falasdinu da aka mamaye.

A Jiya asabar ce kotun ta bada sanarwan cewa tana da hurumin gudanar da bincike da kuma hukunta jami’an gwamnatin HKI kan laifuffukan da suka aikata a yankunan da aka mamaye a shekara 1967 wadanda suka hada da yankunan yamma da kogin Jordan da kuma Gaza.
Har’ila yau kotun zac ta binciki gine-ginen da gwamnatin yahudawan ta yi ba bisa ka’ida ba a kasar Falasdinu da aka mamaye.
Bayan fitar da wannan rahoton Firai ministan kasar, Benyamin Natanyahu ya kira kotun a matsayin kotun siyasa ba na shari’a ba.

Kaduna Press 
7/2/2021

Post a Comment

0 Comments

Close Menu