Kaduna Press
8/2/2021
Da Yammacin Yau Litinin 8/2/2021 Daruruwan Yan uwa Almajirin Sayyed Zakzaky(H) na Da'iran kaduna Sun Sabunta Muzaharan Kira ga Gwamnatin Najeriya ta gaggauta sakin Jagoran Harkan Musulinci a Najeriya wato Sheikh Ibrahim Zakzaky(H) da mai Dakin sa.
Muzaharan ta daga ne da misalin karfe shida 6:00pm na yanma a kan Titin Ibrahim Tayo Road dake kan Ahamdu Bello way kaduna.Yan uwa Maza da Mata ke Dauke da Hoton Malam Zakzaky suna kira ga Gwamnati ta gaggauta sakin Jagoran harkar Musulunci Sayyed Zakzaky da Matarasa Malama Zeenatudin.
Wanda a ke tsare da su tun bayan harin sojojin Najeriya suka kai a garin Zaria ranar 12 ga watan 12 Shekarata 2015, duk cikarsu suna Dauke da Harshashi a Jikin su sama da shekara biyar ba tare da anyi musu magani ba, ko an ciremusu, wanda a halin yanzu haka Uwar gidan Shek Zakzaky Wato Malama Zeenatudin Ibrahim tana dauke da cutar Covid 19a jikinta.
Anyi Muzaharan lafiy an Tashi lafiya.
Kaduna Press
8/2/2021
0 Comments