Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Rouhani: Hukuncin Kotun Duniya Ya Tabbatar Da Ƙarfin Al’ummar Iran Kan Babakeren Amurka

Labaran duniya 
Kaduna Press 
5/2/5022

Jiya Alhamis  Shugaban ƙasar Iran Dakta Hasan Rouhani ya bayyana hukuncin da babban kotun duniya ta Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta fitar kan Amurka a matsayin wata nasara ga al’ummar Iran yana mai bayyana hakan a matsayin alamar da ke nuni da nasara da ƙarfin al’ummar Iran ɗin a kan Amurka.

Shugaba Rouhani ya bayyana hakan ne a yau ɗin nan Alhamis, kwana guda bayan da kotun ta ICJ ta bayyana cewar tana da hurumin sauraran ƙarar da Iran ta shigar kan takunkumin zaluncin da Amurka ta sanya mata bayan da gwamnatin Donald Trump ta fice daga yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma da Iran da kuma sake kakaba mata takunkumin.
Shugaba Rouhani ya bayyana wannan hukuncin da kotun ta yanke a matsayin gagarumar nasara ta ɓangaren shari’a ga al’ummar Iran.
A shekara ta 2018 ne dai Iran ta shigar da ƙara kotun duniyar bayan da Trump ɗin ya sake dawo da takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba wa Iran ɗin a bayan waɗanda kuma aka ɗage su sakamakon cimma yarjejeniyar nukiliyan da kuma ƙara wasu takunkumin na daban waɗanda Iran suka ce yin hakan ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.
A jiya Laraba ce dai babban alƙalin kotun Abdulƙawi Yusuf yayi watsi da kalaman Amurka na cewa kotun ba ta da hurumin sauraren ƙarar ta Iran, inda ya ce kotun za ta saurari ƙarar, lamarin da Amurkan ta bayyana rashin jin daɗinta kan hakan.


Kaduna Press

Post a Comment

0 Comments

Close Menu