Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Sojojin Siriya Sun Kakkaɓo Makamai Masu Linzami Da Isra’ila Ta Harbo Cikin Ƙasar

Labarin duniya
Kaduna Press 
5/2/2021

Makaman kare sararin samaniya na sojojin ƙasar Siriya sun kakkaɓo wasu makamai masu linzami na haramtacciyar ƙasar Isra’ila da aka harbo su cikin ƙasar daga ta ɓangaren yankin Tuddan Golan da Isra’ilan ta mamaye.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar Siriyan ne ya bayyana hakan a yau ɗin nan inda ya ce da misalin ƙarfe 10:42 na daren Shekarn jiya Laraba, sojojin Isra’ila sun kawo hari ƙasar Siriyan daga yankunan Tuddan Golan inda suka harbo wasu makamai masu linzami da ake harbo su daga sama zuwa ƙasa da kuma waɗanda ake harbo su daga ƙasa zuwa ƙasa a wani yanki da ke Kudancin ƙasar ta Siriya.
Kamfanin dillancin labaran ya ci gaba da cewa sai dai dakarun Siriyan sun sami nasarar kakkaɓo waɗannan makamai a yankin Kudu masu yammacin lardin Quneitra da ke Siriyan.
Gidan talabijin ɗin ƙasar Siriya ya nuna wani ɓangaren na kakkaɓo makaman da dakarun Siriyan suka yi.
Wasu majiyoyin sojin Siriyan sun ce an sami nasarar kakkabo mafi yawa daga cikin makaman da aka harbo din duk da cewa wasu sun sauka a wasu wajajen waɗanda ba su yi wata ɓarna ta a zo a gani ba.
Sojojin Isra’ilan dai suna yawan kawo irin waɗannan hare-hare kan dakarun Siriyan da ma na Hizbullah da suke taya su faɗa duk kuwa da cewa hakan bai hana sojojin Siriyan ci gaba da samun nasararori a kan ‘yan ta’addan da Isra’ilan da Amurka suke goya wa baya a Siriyan ba.


Kaduna Press

Post a Comment

0 Comments

Close Menu