Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

​Sudan: A Yau Ne Ake Sa Ran Fitar Da Bayani Kan Kafa Sabuwar Majalisar Ministoci


Labaran duniya 
Kaduna Press 
9/2/2021

Firayi ministan gwamnatin rikon kwarya a kasar Sudan Abdullah Hamduk ya sanar da cewa, a yau ne ake sa ran fitar da bayani kan yadda za a kafa sabuwar gwamnati a kasar.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, bisa bayanan da ofishin firayi ministan kasar Sudan Abdullah Hamduk ya fitar, a yau ne ake sa ran dukkanin bangarori za su kammala mika sunayen ‘yan takararsu domin rike mukamai a majalisar ministocin kasar.
Wannan mataki dai yana zuwa ne bayan rusa majalisar ministocin da firayi ministan na Sudan ya yi a jiya Lahadi, inda ya sanar da cewa dukkanin bangarorin siyasa da ya kamata su mika sunayen ‘yan takarar neman kujerun ministoci, a yau Litinin ne za su kammala mika sunayen nasu.
Firayi ministan gwamnatin rikon kwarya a kasar ta Sudan Abdullah Hamduk ya rusa gwamnatin ne biyo bayan barazanar da shugaban majalisar shugabancin kasar Abdulfattah Burhan ya yi ne, inda ya bayyana cewa idan bangarorin siyasa ba su mika sunayen ‘yan takararsu ba, to zai rusa majalisar ministoci.
Tun bayan faduwar gwamnatin tsohon shugaban kasar ta Sudan Umar Hassan Albashira cikin watan Agustan shekara ta 2019, kasar take fuskantar matsaloli na tatalin arziki, duk kuwa da alkawullan da kasashen turai da na larabawa suka wa kasar, na habbaka tattalin arzkinta.

Kaduna Press

Post a Comment

0 Comments

Close Menu