Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Wasu Yahudawan Sahyuniya Sun Kutsa Kai A Cikin Masallacin Aqsa Mai Alfarma A Jiya Juma'a....

Shafin yada labarai na Palestine Online ya bayar da rahoton cewa,a ci gaba da daukar matakai na tsokana, a yau wasu yahudawan sahyuniya sun kutsa kai a cikin masallacin aqsa mai alfarma.

A cikin kasa da mako guda, yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra'ayi kimanin 436 ne suka kutsa kai a cikin masallacin aqsa mai afamar, da nufin tsokanar musulmi.

A wani labarin kuma wasu yahudawan sun kai wani farmaki a kan yankunan musulmi a gabasin birnin Quds, tare da firgita mazauna yankin.

Baya ga haka kuma sun sauya sunan yankin Jabir da ke gabashin birnin zuwa wani suna na yahudawa, da nufin tabbatar da mamayarsu a kanyankin.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu