A jiya Asabar 06/02/2022 Yan Uwa Mata Almajirin Sayyed Zakzaky na da'iran kaduna Wato (sisters forum) suka Gudanar da mauludin khatama na jerin mauludin da aka Gudanar a Halkoki dake cikin Garin kaduna taron ya gudana ne a un guwar Mu'azu da ke cikin garin kaduna
An gudanar da mauludin ne kamar yadda aka saba, bayan bude taro da Addu'a sai a ka gabatar da Karatun Alkur'ani da ziyarar Sayyada zahra (AS), sai mawakan gidan Manzon Allah suka baje kolin su da wakoki Na yabon Manzon Allah da iyalan gidanshi.
Babban Bako daya halacci wannan taro Shi ne. Sheikh Abdulhamid Bello Zaria ya gabatar da Jawabi na Musamman akan Rayuwar Sayyada zahra (AS) inda yake cewa dalilin da yasa Manzon Allah (SAW) yake kiranta da ummu Abiha sabo da Jarumtarta da jajircewarta da juriya a kan gaskiya dakuma yadda ta tsaya tsayin daka wajen kula da Manzon Allah (SAW) dan haka yan uwa mukara jajircewa a kan riko dasu, dan duk wanda yake bin su toh dole ne ya shirya karbar Jarabawa kala kala, ku duba kuga yadda a kewa Abduljabar baiyi laifin komai ba amma an Rushemai Masallaci, laifin shi shi ne dan yafadi gaskiya da kuma fadin darajar Ahlul-baiti, bayan ya gama jawabi ne
sai mai jawabi Nagaba wakilin yan uwa na Da'irar kaduna Malam Aliyu Umar (Tirmuzi), yayi jawabi a kan Azzalumai da karfafa Yan'uwa dasu dage da Muzaharori a fadin qasarna musamman Abuja da kaduna, ya kuma yi Allah wadai da zalunci da Gwamnatin kano tayiwa sheikh Abbuljabbar Nasiru kabara, dan ya fadi darajan Gidan Annabi a kai masa haka, da man haka hanyar take.
Daga karshe a ka yanka alkaki aka rarraba kyautittika ga wasu Ba'adin Yan uwa wanda ya hada da matan shahidai, da kuma yan Abuja struggle, sai mu'assasatu shuhada'u.
Halkar Imam Hussain shahidin karbala ne tayi biyu (2) da maki 94 da rabi
Halkar Imam Mahadi ne tayi na uku (3) da maki 93.
Bayan kamlawa sai a ka Rufe taro da Addu'a a ka sallami kowa.
Shiga Nan Dan Ganin Hotunan da muka dauko muku a wajan
Kaduna press
0 Comments