Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

​Yemen: Sojoji Da Dakarun Sa Kai Sun Kai Harin Mayar Da Martani Kan Jiragen Yakin Saudiyya


Labaran duniya 
Kaduna Press 
2021-02-10 

Sojojin Yemen da dakarun sa-kai na kabilun larabawan kasar sun kai harin daukar fansa kan wasu jiragen yakin Saudiyya.

Rundunar sojin gwamnatin San’a a kasar Yemen ta sanar da cewa, a yau ta aike da jiragen yaki marassa matuaki guda da suka kai harin ramuwar gayya a kan filin sauka da tashin jiragen sama na Abha a kasar Saudiyya.
Mai magana da yawun rundunar sojin Yemen Birgediya Janar Yahya Sarei ya bayyana cewa, sun harba jiragen marassa matuki ne da nufin tawatsa wasu wurare da ake yin amfani da sua cikin filin sauka da tashin jiragen sama na Abha da ke gundumar Asir a kudancin Saudiyya, wajen kaddamar da hare-hare a kan al’ummar kasar Yemen.
Ya ce da taimakon sun samu nasarar wajen samun dukkanin abubuwan da suka auna, daga ciki kuwa hard a jiragen yaki, kuma a cewarsa wannan na zuwa ne a matsayin mayar da martani kan hare-haren wuce gona da iri da kisan kiyashi da masarautar Al saud take yi kan al’ummar kasar Yemen.
Gwamnatin Saudiyya ta tabbatar da kai harin, ta kuma bayyana cewa ma’aikatan kwana-kwana sun samu nasarar shawo kan gobarar da ta tashi a wurin.
Tun kafin wannan lokacin dai dakarun na Yemen sun gargadi fararen hula a kasar ta Saudiyya, da su guji zuwa wurare na soji da kuma filayen jirgi da ake yin amfani da su wajen kai hari a Yemen.

Kaduna Press 
10/2/2021

Post a Comment

0 Comments

Close Menu