Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, sakamakon hare-haren ta’addanci da aka kaddamar a cikin jahuriyar Nijar, akalla mutane arba’in sun rasa rayukansu wasu da dama kuma sun jikkata.

Rahoton ya ce an kai harin ne a kauyen Tiliya da ke cikin jihar Tawa a kudu maso yammacin kasar a kan iyaka da kasar Mali, yayin da wasu rahotanni suke adadin wadanda suka mutu ya wuce arba’in.

Mako guda kafin haka dai an kai wani harin makamancin wannan, inda akalla mutane 58 suka rasa ryukansu.

Yan ta’adda masu da’awar jihadi ne suke kaddamar da wadannan hare-hare tare da kashe fararen hula da sunan jihadi.