Kd-Press Online
©15/3/2021

A Ranar Asabar din nan 13/3/2021 da ta gabata Dandalin Matasa na da'irar Kaduna Karkashin jagorancin Sayyid Ibrahim Zakzaky, suka gudanar da gidauniya na tallafi ga yar Shaheed Hafeez Dauda.
An shirya wannan gidauniya ne sakamakon yanayi da yarinyan ta ke ciki, na nakasa daya sameta.
Wanan yarinya mahaddacciya ne na alqur'ani mai girma, Kafin wanan lokaci ta kasance tana hawa keke na guragu, amma yanzu girma yazo mata bata Iya hawa keken.
Duba da wanan yasa wannan dandali na matasa shiyar kaduna sukayi kokari na ganin sun saya mata Mashin na hawa.
Wanan gidauniya ya shafi kowani da'ira da halkoki na wanan kasa.
Duba da cewa wanan yarinya kanwa take ga kowani matashi da matashiya, na wanan dandali.
Shi ya sa suka zabi Kaduna ya zama (Central) wajan da wanan gidauniya zai fara, ya yin bude wanan gidauniya Malam Aminu Badiko Ya ja hankalin matasa wajan bayar da gudun mawa mai tsoka, musanman matasan Da'irar Kaduna, duba da irin jajircewar da su keyi na bayar da rai da dukiya lokaci guda, a yayin muzaharori da kuma wasu mauludai.
Shi kuwa Malam Nafiu Sunusi Udawa 
Cewa: ya yi ya zama hakki a kan kowani matshi yayi iyabakin kokarinsa yaga yasauke nasa hakkin kafin lokacin da a ka sanya.

Sai mai mai jawabi na gaba, Ya Allah ka jikan Shaheed Hafeez Dauda, Ya Allah ka amshi aikin da yayi, Sidi Hussain sale, ya baiyana haka ne a lokacin da yake jawabi, sannan ya kara da cewa: hakika Shaheed Hafeez Dauda ya yi kokarin na ganin Matasa sun zama a bun koyi a cikin wanan Al'umma kamar yadda Sayyid Zakzaky (H) ya ke so su zama. Shaheed Hafiz Dauda Harris ne kuma hadimi mai kokari ga jagoran harkar musulunci a Najeriya, yayi shahada ne sakamakon harin sojojin Najeriya a ranar 12/12/2015 a garin Zaria. Kafin shahadarsa ya ba da gudunmuwa sosai a wannan harka, kuma shi ne ya kafa dandalin Matasa, dan cigaban harka islamiyya.

Sign Bashir Kaduna
 Kd-Press Online
©15/3/2021