Sayyid Abdulmalik Alhuthy jagoran kungiyar Ansarullah a kasar Yemen ya bayyana cewa, a cikin shekaru 6 Saudiyya ta rusa masallatai 1400 a Yemen.

Tashar talabijin ta Almasirah daga kasar Yemen ta bayar da rahoton cewa, a cikin jawabin da ya gabatar a ranar Alhamis 25/3/2021 da ta gabata na cika shekaru shida daidai da Saudiyya ta fara kaddamar da yaki kan al’ummar Yemen, Sayyid Abdulmalik Alhuthy jagoran kungiyar Ansarullah ya bayyana cewa, a cikin shekaru 6 Saudiyya ta rusa masallatai 1400 a fadin kasar.

Ya ce tun daga farkon yakin, gwamnatocin kasashen Amurka da Burtaniya gami da Isra’ila suna tare da Saudiyya dari bias dari, kuma tun daga lokacin su ne bata bayanai da kuma taimaka mata wajen kaddamar da yaki kan al’ummar Yemen, tare da yi wa musulmin kasar kisan kiyashi.

Alhuthy ya ce tun daga farko Saudiyya ta yi amfani rahotanni da hukumomin leken asiri na Amurka, Burtaniya da kuma Isra’ila suka ba ta ne wajen kai hari a Yemen, da sunan maido da Hadi Mansur da ya yi murabus a kan mulki domin ya ci gaba da aiwatar da manufofinta a kan al’ummar kasar.

Hakan nan kuma ya bayyana cewa, babu wani dalili na cewa Saudiyya tana fada ne da wani bangare ko wata kungiya a kasar Yemen, domin dukkanin hare-harenta sun shafi al’ummar Yemen ne baki daya.

Masallatai 1400 da Saudiyya ta rusa a Yemen na dukkanin bangarorin al’ummar Yemen ne, haka daruruwan asibitoci, cibiyoyin makamashi, tashoshin jiragen sama da na ruwa, da makarantu da kasuwanni, da madatsun ruwa da gidaje, mafi muni shi ne dubban mutane mata da kananan yara da ta kashe, duk da sunan yaki da wani bangare da ba ta dasawa da shi.

Ya ce abin da ya faru ya kara fito da munafunci na siyasar manyan kasashen duniya, domin kuwa da sun ga dama za su iya dakatar da Saudiyya daga wannan yaki amma ba su yi ba, saboda su ne suke sayar mata da muggan makamai na daruruwan biliyoyin daloli, domin kuwa wata kasa a duniya da za su samu irin wadannan kudade daga wurinta a banza kamar Saudiyya, saboda haka yakin da Saudiyya take yi da kisan dubban fararen hula a Yemen, hakan babbar riba ce a wurin kasashen turai da yahudawa.