Kd-Press Online
21/3/2021

Tashar France 24 ta bayar da rahoton cewa, a zaman da kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya gudanar a ranar juma'a 19/3/2021 da ta gabata, ya bukaci dukkanin bangarorin da suke yaki a kasar da su dakatar da bude wuta.

Dukkanin mambobin kwamitin tsaron sun bukaci da a kawo karshen yakin Yemen, sakamakon asarorin da hakan ya jawo wa al’ummar kasar, wanda hakan yake ci gaba da kara kassara kasar.

A cikin wani bayani da babban sakataren majalisar dinkin duniya ya fitar a jiya, ya bayyana cewa, ci gaba da yakin Yemen zai yi sanadiyyar mutuwar miliyoyin mutane, sakamakon yadda mutane fiye da miliyan 20 suka shiga mawuyacin hali a kasara  yanzu.

Babban sakataren majalisar dinkin duniya ya jaddada cewa, zama kan teburin tattaunawa tsakanin dukkanin bangarori na al’ummar Yemen tare da samo hanyoyin warware matsalar kasar ta hanyar lumana shi ne mafita.

Tun bayan da gwamnatin Saudiyya ta fara kaddamar da yaki kan al’ummar Yemen da sunan yaki da ‘yan Alhuty, kasar ta shiga cikin mawuyacin hali, sakamakon kisan da jiragen yakin Saudiyya suke yi wa fararen hula, tare da rusa gidajen jama’a da sauran cibiyoyi da suke da alaka da rayuwarsu.

Kd-Press Online
21/3/2021