Daga Wajibin Yan Gwagwarmaya a wannan lokacin, dole ne kowannenmu ya dora daga inda Jagoranmu (H) yake wajen kokarin farkar da al'umma hakikanin masu mata ta'addanci da manufar da suke son cimmawa da yin wadannan ta'addan.

Dole ne Malamai da ke Wa'azi su mai da hankali wajen kokarin fadakar da al'umma macutansu cewa su ne wadannan da suke harbinmu da tsakar rana a Titin Abuja, Kaduna da Zaria da ma sauran birane da kauyuka cikin kakinsu na aiki, kuma su ne a lokaci guda suke komawa cikin rigar yan ta'adda sun kashe al'umma a kauyukan Zamfara, Katsina da Kaduna da sauran sassan Nijeriya.

Jagoranmu ya fadi maganar da ba a samu wanda ya musantata ba a hukumance har yau, tabbataccen abu ne cewa hukumar kasar nan ke da hannu a kan hare-hare da yunkurin samar da rashin tsaro a ƙasar nan, kuma su suke Boko Haram ba wani ba! Suna kuma yi ne da umurnin iyayen gidansu na waje, wadanda suke shirya abubuwa suke turo da makamai don a sanar da yanayin da za su shigo kasar da sunan kawo zaman lafiya da ba da tsaro, sai su mamaye kasar daga nan. Abin da suka kira 'second scramble of Africa'.

Ba maraba tsakanin abin da aka kira Boko Haram da wadannan da yanzu ake kira Barayi ko Yan Ta'adda ko Masu Garkuwa da Mutane. Duk cikarsu aiki iri daya suke yi, Kisan kai kawai ba ki ba gani, ba gaira ba dalili. Aiki iri daya suke yi, da makamai iri daya suke amfani, kuma daga tushe guda suke samo makamai da kudin da suke aikin da umurnin aikin ma. Abu guda ne, kuma hadafi ko manufarsu daya ne, ba bambanci.

Al'umma su gane, azzaluman mahukuntan kasar nan su ke kashe su a sumummuke! Jami'an tsaron da ke kashe yan gwagwarmaya da tsakar rana suna sanye da kaki kowa na gani. A lokacin guda da daddare su ke sauya kama su kai hare-hare da sunan yan Ta'adda, su ne 'yan ta'addan ba wasu ba. Su ke ta'addancin.

Idan yan gwagwarmaya suka ma al'umma shiru kan halin da ake ciki, tabbas za a wayi gari mutanen nan sun cinye kasar nan da yaki. Tunda sun kulle Shaikh Zakzaky suna ganin ba wata muryar da za ta fadakar ko ta tona asirin kulle-kullensu, bai kamata almajiran Shaikh Zakzaky su yi shiru ba. Hakki ne kanmu mu yi ta fadawa mutane cewa hukumar kasar nan, wadannan shugabannin da ke iko azzalumai ne, miyagu ne, tsinannu ne, kuma duk halin kuncin da ake shiga, su ne dalilinsa. Kuma ba wata mafita illa ai musu bara'a, a mika Wila'a ga Allah (T) da addininsa.

Allah Ya mana maganin azzalumai.