A shekarar bana an dauki kwaran matakai dangane da buda baki a masallacin haramin Makka mai alfarma da masallacin manzon Allah (SAW) sakamakon yaduwar cutar coruna, da kuma yadda za a dakile yaduwar wannan cuta ta hanyoyi daban-daban, daga ciki har da takaita yawan mutane a wadannan wurare masu tsarki da kuma bayar da tazara, gami da sauran matakai na tsafta.