Cibiyar fikihun muslunci ta duniya ta bayar da fatawar cewa, allurar rigakafin cutar corona ba ta karya azumi.

Shafin yada labarai na Almadina ya bayar da rahoton cewa, cibiyar fikihun muslunci ta duniya ta bayar da fatawar cewa, allurar rigakafin cutar corona da aka yi wa mutum ta karkashin fatarsa ko a cinya ba ta karya azumi.