Wakilin jami'ar Almustafa a yankin tsakiyar asia Mohsen Dadsarasht ya bayyana cewa, ayyukan ibada da suke cikin watan ramadan tsari ne ga dukkanin sauran kwanakin rayuwarsa, wanda idan ya bi su zai samu kamala a cikin rayuwarsa.

A cikin bayanin da yake gabatarwa wanda ake sakawa a cikin faifan bidiyo da ake watsawa a wasu kafofin yada labarai, malamin ya bayyana cewa, manufar tarbiyantar da ruhi da jikin dan adam a cikin watan bisa bautar Allah, ita ce domin jikin ya saba kuma ya ci gaba haka a sauran rayuwarsa.

Ya ce azumi na nafila da sauran ayyukan nafila da ake yi a watanni da ba na ramadan ba, suna a matsayin ci gaba ne na ayyukan da aka fara daga watan domin dan adam ya mayar da ibada cikin tsarin rayuwarsa ta yau da kullum ba sai cikin ramadan ba.