Kd-press Online
©16/4/2021

Da yammaci yau Juma'a 16 ga watan 4 Shekarar 2021 da misalin karfe 6:00pm dai-dai na yamma a kan titin Nnamdi Azikiwe Express Bypass, daura da Kabala Junction, Kaduna. daruruwa yan'uwa Musulmi Almajiran Sheikh Zakzaky, na garin Kaduna sun fito domin cigaba da yin kira ga gwamnatin  Najeriya da ta sakin jagoran harkar Musulunci a Najeriya Sheikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa, wanda da take cigaba da tsarewa tsawon shekaru fiye da biyar ba tare da laifin komai ba.


Sai kafin a kai yin da za a kulle wannan muzahara, da zuwa kagoro junction daura da GT Bank jami'an yan sanda tare da hadin gwiwar yan kato da gora, sun kai wa masu muzahar hari, batare da wani dalili ba. 

Harkar musulunci a Najeriya ya dade yana fuskantar takura da tsangwama da ga masu tafi da Mulkin kasar.


Sai dai al'amarin ya fi tsananta ne tun bayan harin sojojin najeriya da suka kai a kan 'yan uwa musulmi na Harkar Musulunci a Najeriya (Islamic Movement in Nigeria) a watan Disambar ranar 12/12/2015, tin ga wannan ranar ne almajiran Sheikh zakzaky ke fuskantar takura, cin zarafi da wulakanci, daga jami'an tsaron kasar nan tare da hadin gwiwar zauna gari banza, karkashin jagorancin masu tafi da iko, ta han yar take hakkin su, da hana su yin addini yadda suka fahimta a matsayin na 'yan Nigeria,

haka al'amarin yake tafiya, jami'an tsaro na kai hare-hare a kan su lokaci bayan lokaci, a lokutan muzaharori da sauran munasabobi, a fadin kasan nan.

Zuwa hada wannan rahoto dai a kwai tabbacin an samu mutun biyar wadan da jami'an yan sanda suka raunata.

Kd-press Online
©16/4/2021