Yau Litinin 19 Ga watan Aprilu yake alamta Shekaru 28 da fara sheƙar da jinanen yan uwa Musulmi almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky (H). Waki'ar wanda ta faru a garin Katsina bayan an fito wata Muzahara a ranar 19 ga watan April na shekarar 1991 domin nuna rashin amincewa da ɓatanci da wata Jarida Mallakin gwamnatin Najeriya tayi.

 A irin wannan rana yan uwa Musulmi sun fito Muzahara a duk faɗin ƙasar nan domin nuna rashin amincewarsu akan cin zarafin da wannan jaridar tayi ga Manzon Allah (S) inda har yan uwa suka ƙona copy na Jaridar a yayin Muzaharar. A ko ina an kammala Muzaharar lafiya amma a Katsina bayan an kammala sai gwamnan Soja na lokacin mai suna Yohanna John Madaki ya fito a kafafen watsa labarai yana cewa "Idan aka ƙara Irin wannan zanga-zangar zai tafi har gidan Sheikh Yaƙoub Yahaya ya kamo shi ya kai shi har filin Polo ya harbe shi".

  Wannan kalaman da John Madaki yayi yasa Sheikh Zakzaky yazo har nan Katsina domin jan kunne ga shi Yohanna John Madaki, sannan kuma ya taya Sheikh Yakubu Yahaya murnar wannan babban matsayi da ake masa barazana da ita na samun Shahada, har Sheikh Zakzaky yake kiran Malam Yakubu Yahaya da gwarzon kare Martabar Manzon Allah (S).

 Bayan Sheikh Zakzaky (H) ya gama jawabin jan kunne ga John Madaki. Sannan ya bada umarni cewa a sake wata Muzaharar ranar Juma'a da zata zo a wanann satin. Wannan yasa hukuma ta shirya sosai domin  dirarwa yan uwa da nufin ganin cewa ba ayi wannan Muzaharar ba, ko kuma a lokacin da ake Muzaharar su afkawa Muzaharar. Idar da sallar Juma'a keda wuya sai yan uwa suka hau sahu aka fara Muzahara, a dai-dai wani waje da ake kira Kasuwar Gwangwan sai jami'an tsaron ƴan sanda suka fara Harbo tiyagas da kuma dukan yan uwa da sanduna.

 Kusan a wannan waƙi'ar ne aka fara samun Shahidi a wannan Harka da Sheikh Zakzaky yake hjagoranta. Kuma wannan waƙi'ar ta 19 April 1991 daga ita ne Sheikh Zakzaky (H) ya assasa Yaumu-Shahada. Yau waƙi'ar tana da shekaru 28 kenan, wanda suka aukar da ita sun ƙaskanta wasu basu nan amma Harka Islamiyya na cigaba da gudana.

 - Ibrahim Almustapha Saminaka
 - 19/Aprilu/2021