Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

ANGUDANAR DA MUZAHARAN 🇰🇼QUDUS TARE DA FREE ZAKZAKY A DA'IRAR KADUNA.....

ANGUDANAR  DA MUZAHARAN 🇰🇼QUDUS TARE DA FREE ZAKZAKY A DA'IRAR KADUNA.....

Kaduna Press✍🏼
7/5/2021
Dubbannin Almajiran Sayyid Zakzaky ne suka fito domin nuna goyan bayan su ga al'umar Palatine tare da kira a saki jagorar Harkar Musulunci Sheikh Zakzaky da mai dakin sa, a yau juma'a 7/5/2021 a da'irar kaduna.
Masallacin Qudus (Al-Aksa ko Baitul-Mukaddas) ya kasance al-Kibla ta farko ga Musulmi, Masallaci na 3 mafi daraja bayan Ka’abah (mai girma) da Masallacin Annabi Muhammad(saw) da ke garin Madinah.

Palasdinu; wuri ne da aka saukarwa Annabawa(as) wahayi, cibiyar addinan da Allah ya saukar, kuma albarka tana kewaye da ita ta ko’ina. Bugu da kari, Palasdinu wani yanki ne na tarihin Musulmi, doriya akan kasancewarsa Masallacin Qudus alkiblar musulmi ta farko da kuma gurin da Annabi Muhammad(saw) yayi Isra’i kafin Mi’iraji, yayinda Annabi(saw) ya jagoranci Annabawa(as) sallah a masallacin Qudus.

Ranar Jumu’a ta karshe ta ko wane watan Ramadan; rana ce da marigayi Imam Khomeini(qs) ya ware a matsayin Ranar Qudus ta duniya; tun a shekara ta 1979 (shekarar farko bayan cin nasarar juyin musulunci a Iran).

Don haka, a ranar Qudus, dukkanin al’ummar musulmi ke fitowa; kwan su da kwarkwatar su, don nuna goyon baya ga Palasdinawa da ake zalunta da kuma yin tir da Allah waddai da ta’addancin Yahudawan Sahayoniya.

Imam Khomeini(qs) ya kasance mai neman hakkin alummar Palasdinu da kyamar mamayan Yahudawan Sahayoniya ga Palasdinu tun shekaru masu yawa kafin cin nasarar juyin musulunci a Iran. Bayan da aka sami nasar juyin musulunci farkon aikin da Imam(qs) ya fara yi game da wannan dadadden tunani na shi. 

Shine rufe ofishin jakadancin haramtacciyar kasar Israila da kuma mika ofishin nasu ga masu gwagwarmayar ‘yantar da Palasdinu.

Al hamdulillah Yan uwa Almajiran Sayyid Zakzaky na Da'irar Kaduna ba a barsu a baya ba sun amsa wannan kira,


_Kaduna Press.✍️
Today.. Friday 07/05/2021.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu