Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

CIGABA DA ZIYARAN GIDAJEN SHAHEEDAI A KADUNA

Wakilin yan uwa almajiran Sayyid Ibrahim  Zakzaky(H) na garin Kaduna Malam Aliyu Umar (Tirmizi) yakai ziyara jiya litini 17 /5/2021 wanda yayi daidai da 6 ga watan Shawwal 1442 Halkar Shahidin Karbala Imam Hussain (AS). 
Anfara ziyaran ne da gidan Shaheed Muhammad Auwal (Mabo) wanda yayi shahada a Gyallesu Zariya. Shaheed Muhammad Auwal (Mabo)  shine wanda ke jagorantan kwamitin masu (welder) na wanan harkan bugu da kari kuma tsayayen Haris ne mai kokarin gaske.
Gidan na biyu kuma shine gidansu Shaheed Jawwad Aminu Liman, Shaheed Jawwad matashi ne kuma dan Mu'assatul Abulfadal Abbas,  yayi shahada ne a muzaharan Free Zakzaky a junction na bakin Ruwa Kaduna. 
Sannan aka zarce gidan su Shaheed Ibrahim K/mashi Shima yayi Shahada ne a Muzahar Ashura, a nan Junction na Bakin Ruwa, daga nan sai gidan Malam Ibrahim ( Badikko). 
 A yayin ziyaran Malam Aliyu Tirmizi yayi kira ga iyalan Shaheedan da sukara hakuri da wannan  yanayi da suka samu kansu a ciki na maraici, sannan ita Shahada karama ce bako wane yakan samu ba .
 Mun godema Allah da yasa yan uwan mu an zubda jinanansu ne bisa zalinci ba wani laifi sukayi ba, sai dan sun ce: dan sunce Ubangijin su  shi ne Allah kuma shi zasu bi.
Muyi duba ga wasu dasuke rasa rayukansu akan wasu harkoki na sharholiyan duniya Sannan yayi kira ga ya'yan Shaheedan da su tsayu a kan turban da iyayansu suka barsu a kai kuma su zama jakadu nagari a cikin wanan alumma musanman wurin neman ilimi da kuma aiki dashi. 

Ga kadan daga hotunan damuka dauko muku ______________

Kaduna press
©17 /5/2021

Post a Comment

0 Comments

Close Menu