Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

GWABNATIN JIHAR KADUNA: TABARMAR KUNYA DA HAUKA AKE NADE TA.

1, Maganar sababbin tuhume-tuhume, tabarmar kunya ce.
2, Maganar daukaka kara, ba  tana nufin dakatar da sakin da kotu tayi ba. Donhaka ba matsala ba ce. Tabarmar kunya ce.

ABIN DARIYA WAI YARO YA TSINCI HAKORI

By Ishaq Adam Ishaq Esq.
 31 July,2021.

SABABBIN TUHUME-TUHUME.

Mungani a kafafen yada labarai cewa, wai gwabnatin jihar Kaduna ta shigar da wasu sababbin tuhume-tuhume a gaban Babbar kotun Tarayya dake  Kaduna,bayan sun sha mummunan kayen da suka suma. To wannan tabarmar kunya ce. 

Idan ma da gaske ne sun shigar da wasu sabbin tuhume-tuhume, to mu bamu gansu ba. Kuma baza su iya dakatar da hukuncin da babbar kotun jihar Kaduna ba,na sakin su Sayyid Ibrahim Zakzaky(H) da tayi. 

DALILI KUWA SHI NE:

1 Alkalan Babbar kotun Tarayya dake Kadunan sun tafi hutu tun sati biyu da suka wuce, kuma baza su dawo ba sai nan da  wata 2 masu zuwa. Donhaka basuga takaddar ba, basu samata hannu ba, basu sanya date ko ranar da za,a fara sauraron karar ba. Haka kuma Su Sayyid ba,a basu ta kaddar tuhumar ba,lauyoyin su ma ba,a bamu takaddar tuhumar ba. Kuma ko sun bada, idan babu sahannun alkali, daidai take da takaddar kunshe kosai ko tsire. 

Donhaka jami,an tsaro kuwa wadanda ba,a karkashin ikon El-rufa'i suke ba, zasuyi aiki ne da hukuncin da babbar kotun jihar Kaduna din tayanke ne, wanda ya sanya El-rufa'i ciwon kai da rudewa.

Sun qi, Allah yaso kuma na Allah shine gaskiya. Kawai dole su yadda sun sha kaye. Tun farko sun sancewa,basu da case. Amma sukai ta yaudarar al-umma. To yaudara na da karshe.

MAGANAR DAUKAKA KARA.

Wannan kalmace ta gama-gari,wadda kowa ya saba jinta. Idan mutum yana zuwa kotu, zaiji duklokacin da kotu ta yanke hukunci ta kance, dun wanda hukuncin bai  yi mishi dadi ba, yana iya daukaka kara zuwa kotun gaba. Dokar kasa ta bashi da damar yin hakan.

Amma ko da sun daukaka kara,ga yadda abin yake;

1, Bazai dakatar da sakin su Sayyid(H)da kotu tayi ba.

2, Su Sayyid ma baza su ringa halartar zaman kotun ba.

3, Lauyoyin su Sayyid da na gwabnati ne zasu ringa haduwa muna qwamawa a gaban kotun.

Idan suka daukaka kara, tabbas kunya zasu sake sha. Domin Kotun daukaka kara, bawai zata fara shariar daga farko kamar yadda wannan kotun tayi ba. Zata karbi coping shariar ne taga yadda a kayi shari,ar tun daga ranar farko har zuwa ranar karshe, sannan tayi nata hukuncin. Donhaka tabbas itama za tabi sahun wannan kotun ne.

Lokacin da Babbar kotun jihar Kaduna ta saki 'yan uwa na waqi,ar Zaria, Kwamishinan sharia da lauyoyin gwabnatin Kaduna sunyi taron manema labarai,sukace zasu daukaka kara. Amma izuwa yanzu kusan shekara biyu, basu daukaka karar ba. Haryanzu ba su bamu abin da ake kira da NOTIC OF APPEAL(takaddar daukaka kara) ba.

Zasu iya fadin cewa zasu daukaka kara domin su birge mai gidansu El-rufa'i, Kuma domin a sami damar diban kudin al-ummah. Shi wanda ya ce zasu daukaka karadin da za,ace da kudin aljihun shi za,ayi amfani wajen daukaka karar,to bazai yadda ba, sabida yasan bazasuyi nasara ba har abada. 

Donhaka indai daukaka kara ne, ba matsala ba ne. Muna nan muna jiran su.

Sunyi hakane domin su karkatar da zukatan al-umma daga farincikin da sukaga 'yan Nigeria da Kasashen waje sukeyi. Basu zaci irin wannan yawan masu murna ba. Sundauka iya mu almajiran Su sayyid ne kawai zamuyi murna. To cikin masuyin murnar har aljanu a kwai.

Donhaka al-umma su kwantar da hankalinsu. Mu cigaba da murna da farin ciki na sakin jagoran gaskiya wanda aka zalunta. Gaskiya ce ta farayin halinta.

Allah ka kare mana su allamah Sayyid Ibrahim Zakzaky(H) a duk inda suke.

Via Legal highlight & opinion s.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu