Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

SADAUKARWA DA RIKO DA SHUGABA

 Kaduna Press
©18/8/2021

A Ranar 9 ga watan Muharram, ranar Tasu'a, a rana mai kamar ta yau, shekaru 61 bayan hijirar Ma'aiki (s) Shimr bn Zil Jawshan, daya daga cikin manyan kwamandojin Yazid a Karbala (wanda kuma yake matsayin kawu ga Abul Fadhl al-Abbas), ya nemi ya bai wa Abbas da sauran 'yan'uwansa ta wajen mahaifiyarsu Ummul Banin, wato Abdullah, Ja'afar da Usman, lamuni da kariya matukar za su juya wa Imam Husain (a.s) baya.

Lamarin dai ya faru ne lokacin da Shimr ya taho sansanin Imam Husain (a.s) ya ce: "Ina 'ya'yan 'yar'uwata, wato Abbas, Abdullah, Ja'afar da Usman? Amma ba su amsa masa ba har sai lokacin da Imam Husaini (a.s) ya ce wa Abbas: "Ka amsa masa mana ko da dai fasiki ne, amma ai yana daga cikin kawunanku". Sai Abbas ya ce masa: "Me kake so"? Sai ya ce: " Ya ku 'ya'yan yar'uwata kuna cikin aminci, na bukaci kariya gare ku daga Ibn Ziyad, amma me ya sa kuke son kashe kanku tare da Husain? Me zai hana ba za ku shigo cikin dakarun Yazid ba? Nan take sai Abbas ya amsa masa da cewa: Allah Ya la'ance ka, Ya kuma la'anci kariyarka,  shin za ka ba mu kariya ne alhali dan Manzon Allah ba shi da kariya?!

Wannan daya ne daga cikin irin jaruntaka da kuma sadaukarwar Abdul Fadhl al-Abbas (a.s)  ga dan'uwansa kuma Imaminsa, Imam Husain (a.s).

 Kaduna Press
©18/8/2021

Post a Comment

0 Comments

Close Menu