Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Yadda Aka Gudanar Da Muzaharar Ashura Ta A Da'irar Kaduna...

Kaduna Press
©19/8/2021

A yau Alhamis 19 ga watan 8 Shekar 2021 dai-dai da 10 ga watan Muharram Shekarar 1443 'yan uwa Musulmi Almajiran Shaikh Zakzaky (H) na garin kaduna suka gudanar da Muzaharar Ashura, da Misalin karfe 2:00pm na Rana.
Kamar yadda a ka saba duk Shekara 'yan uwa Almajiran Shaikh Zakzaky (H) na garin Kaduna, da ma sauran yan uwa na Kasar (Najeriya) suna gudanar da wannan Muzaharar ta tunawa da Mazlumiyyar da a kayiwa Aba Abdullahil Hussain (As) jikan Manzon Allah (S) wacce aka fi sa ni da "Muzaharar Ashura" a wannan Shekarar ma Almajiran Sayyid Zakzaky na garin Kaduna sun bi sahun takwarorin su na sauran garuruwa, duk da mumunar shirin gwamnatin kaduna.
An tada Muzaharar ne daga jama'a road kawo Kaduna, in da tayi tafiya mai tsawo tabi ta gefen gadar kawo ta nufi hanyar rafin guza, ta shiga cikin kasuwa,

Alhamdulillah sannan muzahara ta isar da Saqo, musamman anyi a in da ba a saba yi ba, da wasu labari suke ji, yau sun gani da idon su, koma sun nuna alhinin su game da musa'ib din da ya samu Ahli Muhammad (S).

Daga karshe dai yayi Addu'a a ka Sallami kowa.

ANYI LAFIYA ANTASHI LAFIYA.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu