Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

LAJNAR ASHURA DA TATTAKIN ARBAEN NA IMAM HUSAIN (AS) NA HARKAN MUSULUNCI A NIGERIA KARKASHIN JAGORANCIN SHAIKH IBRAHIM ZAKZAKY (H), BITAR PROGRAM DIN ASHURA TARE SHIRIN TATTAKI DA ZAMAN WAHADA


Lahadi 27/1/1443H dai dai da 5/9/2021

To bazamu iya kawo dikkan a bin da ya gudana awajen ba, amma zamu so, mu dan yi tambihi ga al'umma da suke kallo daga gefe, da su kan su masu tattaki.

KADAN DAGA CIKIN MANUFAR TATTAKI

Da farkio dai yana da kyau mu gane cewa: Waki’ar Ashura Yunkuri Ne Na Kau Da Gidan Manzon Allah (S), wanda kuma sakamakon wannan musiba har yanzu al’umma tana fama da shi, tana fama da wannan sakamako, na yunkuri na ganin cewa an karakar da gidan Manzon Allah (S), domin a tabbatar da cewa addinin wannan Manzo ya kawo karshe. Wannan a sarari yake a bayanan da Yazidu ya yi a yayin da aka kai masa kan Husaini (AS).

Muna Wannan tattakin ne domin rayayar da Addini da jajantawa Manzon Allah (saw) na irin abinda ya sami lyalan gidansa tsarkaka na Kisan gillah da'akayi musu a hannun makiya Allah (swt), a Shekara ta sittin da Daya (61) bayan hijira Manzon Allah, Annabi Muhammad (saw). Wannan tattakin ramzine na irin wahalhalu da lyalan Manzon Allah (saw) suka fuskanta na tattaki tun daga inda akayi musu Wannan Kisan gillan, ma'ana Karbala!!! dake kasar lraqi zuwa Sham fadar mulki na wancen lokaci dake Kasar Siriya ta yanzu kama-kama har zuwa birnin Manzon Allah (saw) (Madinatun Nabiy) dake Daular Saudi Arabia ta yanzu.

Wannan Jajantawar ta ha

r Abada ce babu ranar yankewa. Kamar yadda lmam Ali Al-Ridha yake cewa:

"Wanda ldanuwansa suka zubar da hawaye, Kuma yayi kuka akan musibar data same mu daga makiyanmu, Allah zai tayar dashi a cikin jama'armu. (Yace) Ya! Da'abal (Sahabin lman Ridha ne), Wanda yayi kuka akan musibar kaka Na Hussain (as) Allah ya gafarta masa zunubban Sa gaba daya"

                       TANBIHEE:
Yana da kyau Al'umma su gane manufar tattaki, amsawa kiran lmam Hussain (as) ne, da yayi a lokacin daya rage saura shi daya gaban dubban makiya Yana Kiran cewa: HALMIN NASIRIN YANSURUNA?!!!, Shine ka amsa da Wannan tattakin kace: LABBAIKA YA HUSSAIN, LABBAIKA YA HUSSAIN, LABBAIKA YA HUSSAIN!!!

*ABIN DA YA KAMATA ME TATTAKI YA LURA DASHI MUSAMMAN AWURIN TATTAKIN.*

*1.HADAFI:* Yana da gayan muhimmanci masu tattaki su sani cewa Wannan aiki da Sukeyi neman kawo gyarane a cikin Al'ummar Manzon Allah (saw). Ba mun fito bane don nunawa mutane cewa muna dayawa bane ko don mu fusata su. Manufar ta zama yadda shi kanSa lmam Hussain (as) yafada yayin fitarSa, inda yake cewa:

"Ban fita Ina Mai girman Kai ko asharari ba, Nafita ne domin neman kawo gyara acikin Al'ummar kakaNa Manzon Allah (saw).

Ina son inyi umurni da kyakkyawa, Kuma nayi hani da Mummuna, Kuma ina son in tafi a irin matafiyar kakaNa Manzon Allah (saw)" da Kuma Mahifina Ali dan Abi Talib (as)"

*2.IKHLASI:* Wani abu dake zama mizani a wurin Allah, shine yi don Allah. Da zarar an rasa Wannan, to dukkan ayyuka ba a bakin komai Duke ba wurin Allah (swt). kamar yanda malamai suka jawo hankali a wajan sanan suka tunatar da yan uwa maganan Jagora cewa: a yafi juna ayi aiki tare.

Shiwanan aiki ba albashi ake bayarwa ba kuma ba mukami bane balle kace wane yataremun gaba yaki bani dama matsayina ya hauhawa, bill hasalima nagaba shi yafi shan wahala .missali yanzu muyi duba ga jagora duk cikin mu wayakaishi shan wahala?.

*3.lLIMI:* Abin nufi da ilimi anan; shine cikakken masaniya akan abinda kake kokarin bada umurni akan sa, ko Kuma kake kokarin hanawa. Anan ana nufin kiyaye fadin abinda baka da ilimi akansa. Sannan karda ka shiga aikin da banaka ba, ka tsaya in da aka ajeye ka.

*4.JURIYA DA HAKURI:* Manufa anan itace, a matsayinka na me tattaki ka sani Kai me isar da sakon Manzon Allah da lyalan gidansa  tsarkaka na halin da suka shiga na tsanance-tsanance da wahalhalu, Kamar irinsu zagi, duka, harma da kisa, to dole ne kaima ka nuna irin wannan jarumtakar da hakuri a yayin da  kaci karo dasu, ta yiwu wani yayi maka shigen ire-iren abun da iyalan gidan Manzon  Allah suka fuskanta, to kai ma ka fuskance shi da hakuri da yafiya, a lokaci guda Kuma kana tuna irin juriyar da Sayyida Zainab Al-Kubra Aqeelatu Bani Hashim, da lmam Ali Zainul Abideen (as) da saura ahlinsu, sukayi a yayin da suka tsinci kansu a hannun makiya.

*5.SHIGA TA KAMALA:* Wajibi ne mai tattaki ya kiyaye irin shigarsa, ma'ana irin suturar daya kamata yasa domin fuskantar irin mutanen da yake son isarma sako, Wannan ya hada harda salon aski ga matasa.

*6.TSAFTA:* A Wannan tattakin ana sa ran za'ayi shine cikin Ruwan sama da  Sanyi da iska Wanda mai tattaki yakamata yatanaji kayan sanyi da facemask da hand sanitezer dakuma rigan ruwa  ,wani abu dayake da muhimmanci kula da tsaftar jiki dana tufafi.

Kaduna Press

@5/9/2021

Post a Comment

0 Comments

Close Menu