A yau Laraba 12/10/2021 da musalin karfe 12:00pm na rana yan uwa musulmi almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky na halkar Amirul Muminin kaduna, sun gudanar da maulidin fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S).
Bayan bude taro da addu'ah da karatun alqur'ani sai a ka shiga fagen sha'irai, sannan a ka karanta ziyarar Annabi (S) sai a ka gabatar da mai jawabi Wakilin yan uwa na yankin kaduna Malam Aliyu Umar (Tirmizi) Malam ya fara da yiwa Allah godiya tare da taya yan uwa murnan zagayowar watan da a ka haifi Annabin Rahma (S), sannan ya kara da cewa: mun tsinci ka mu a cikin al'ummar da ba ta san waye Manzon Allah ba. Maulidi ba wai a nayin ne dan a hadu da juna ba kwai, ana koyar da darrusa ne daga dabi'un Annabi (S), wannan kuma shine manufar jagora Sayyid Ibrahim Zakzaky.
Malam ya cigaba da kawo lalar Annabi (S) da kyawawan dabi'unSa a karshe Malam yayi kira ga Yan uwa da su zama kyawawa jakada ga wannan harka, ta hanyar koyi da rayuwar Manzon Allah, Annabi Muhammad (S).

Daga karshe an raba walima, aka yanka Alkaki, sannan akayi addu'ah a ka sallami kowa.