Har yanzu, Jaridar ALMIZAN ita ce babbar kafa (Medium) na taskancewa da adana bayanan Harkar Musulunci, musamman labaran yau da kullum da ke fitowa daga kowane lungu da sakon fadin Da'irorin Harkar nan.

Ita ce kafa mafi inganci da Harka ke da ita a fagen samowa da yada rahotonnin aikace-aikacenta da harkokinta.

Ko da yake ba lallai ne komai da ke cikinta ya zama ya dace 100% da ra'ayin Harkar Musulunci ba, kasancewarta Jarida da ke shiga hannun kowa da nufin isar da sako, fadakarwa da ilmantarwa, amma tana iyakan kokarinta ya zama ba ta yi hannun riga da ra'ayin Harkar ba face sai da kuskuren da bisa kuskure ya auku.

ALMIZAN kundi ne babba na adana Tarihin Harkar Musulunci a tsawon shekarunta fiye da 30 zuwa yanzu. Don haka ya dace kwarai kowane dan uwa da yar uwa a daidaiku ko a jumlace su himmatu wajen ba ta gudummawar da duk suke iyawa, na aiki ne ko tallafin kudi don cigabanta.

Mafi karancin gudummawar da Da'irori za su rika ba ALMIZAN shine su rika bata tallar buga hotunan tarurruka da ayyukan Da'ira da Halkokinta. Haka ma Lajanoni da Mu'assasoshin Harka.

Duk labarin da ba a Wallafa shi a Almizan ba, daidai yake da ya faru ya gushe a kundin Tarihin Harkar Musulunci, matukar ba an buga shi a wani littafi bane wanda ya yadu ya kuma taskatu fiye da jaridar.

Mu muhimmanta Almizan a daidaikunmu ta hanyar sayen kwafinta a kowane mako, tare da ba da sanarwar tarurrukan bukukuwa, aure, kasuwanci da 'programs' dinmu da muke yi yau da kullum.

ALMIZAN Itace Jaridar Hausa da ta fi kowacce jarida shiga sako da lungun kasar nan da wajenta.