kaduna press
 19/10/2021

A yau talata 12 ga rabiul auwal, wanda yayi dai dai da 19/9/2021. Dandazan masoya Annabi Muhammad (s.a.w) sun gudanar da taron tunawa da watan da a ka samu Fiyayyan Haltta Annabi Muhammad (S) a garin kaduna.
Makarantun islamiyoyi da sauran Sha'irai, damasu nuna bajinta takowani bangare, sunnuna iyakan kurewan soyayan su ga shugaban hallita, suma yan uwa musulmi Almajiran Sayyed Zakzaky (H), ba a barsu a baya ba domin makarantun fudiyoyi da dama sun samu halarta sanan sun birge kowa dayake muhallin maulud din. Da isowarsu wajan sai kallo yakoma sama sabo da sallon faretin girmamawa da su keyi ma Annabi Muhammad (s .a .w.w) Yasha banban da Wanda jama'a suka Saba gani yau da kullin, sai kawai kaji wajan ya dauki kabbara, jama'a dama sun yaba da iron tsarin da yan shi'a suke da shi, na rashin yamutsi tsakanin maza damata.
Taron yasamu hallartan manyan mutane da ga kowani janibi, kama daga sarakunan gargajiya da manyan ma'aikan gamnati da yan kasuwa, da sauran su.
Kuma cikin yardan Allah anyi lafiya antashi lafiya.

Kaduna press
RADIO&TV
©19/10/2021.