Ajiya Lahadi 31/10/2021 makarantar Fatimatuz-Zahra (s.a) suka gudanar da bikin yaye dalibai 19. Taron ya halartar mutane dadama  da ga janibobi daban- daban. Daga ciki a kwai Pastor Yohana Buru, wakilin yan uwa almajiran Sayyid zakzaky na garin Kaduna, Malam Aliyu Umar (Tirmizi) tare da Sharif Shubuli Kano, wanda shine babban bako mai jawabi a taron,

Sharif Shubuli ya fadakar da jama'a a kan mahimmancin neman ilimi, in da ya bayyana cewa: yakamata yan uwa musulmi su ba da himma wajen magance matsalar ilimi acikin gidajenSu, da kuma Al'umma gaba daya, yakuma kara da cewa: dole ne iyayen yara su dau Al"marin malaman makaratun Islamiyya da muhimmanci, san nan yayi takaitaccen jawabi akan Annabi (s.a.w).
Bayan ya Sharif Shubuli ya kammala sai a ka gabatar da Pastor Yohana Buru, inda ya yi jawabi a takaice a kan muhimmanci ilimi da rawar da ilimi ke takawa a duniya, tare da nasiha ga al'umar musulmi da na kirista.

Sannan a ka mika a bin magana ga wakilin yan uwa na garin Kaduna Malam Aliyu (Tirmizi) yayi jawabi a takaice, sai a ka bawa yan sauka shahadar su gamida  kyaututtuka, sannan a kayi addu'a a ka sallami kowa. 

Da fatan Allah yayima karatu albarka

#KadunaPress
©1/11/2021